Mai Martaba Sarkin Kano Ya Bukaci Kungiyar Matan Yan Sanda (POWA) Su Kara Himma Wajen Koyar Da Marayu Sana’o’in Dogaro Da Kai.

Spread the love

Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero CFR.JP , ya bukaci kungiyoyin matan yan sandan Nigeria da su kara himma wajen hada kan kungiyar matan yan sandan domin koyawa marayu da masu bukata ta musamman sana’oin dogaro da kansu.

Mai Martaba Sarkin Kano,ya bukaci hakan ne lokacin da kungiyar Matan yan sanda reshen jihar kano, Police Officers Wives Association(POWA) suka kai masa ziyara a fadar sa.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce yaji dadin ziyarar da kungiya Matan yan sanda suka kawo masa tare da kudiurin da suke dashi na taimakawa marayu don su dogara da Kansu ba sai gwamnati ta basu aikin yi ba.

A nata jawabin Shugabar Kungiyar kuma Matar Kwamishinan Yan Sandan jihar Kano, Hajiya Aisha Muhammed Usaini Gumel ta ce ta zo fadar Sarkin ne domin nuna goyon bayanta ga masarauta da kuma basu shawarwari domin ci gaban kungiyarsu.

A wani ci gaban kuma Mai Martaba sarkin na Kano ya kai ziyara asibitin Murtala Muhammed, dake cikin birnin Kano domin duba marasa lafiya wadanda wani matashi ya bankawa wuta a massalaci a dai dai lokacin da suke gabatar da sallar asuba garin gadam dake Larabar Abasawa a karamar hukumar gezawa.

Alhaji Aminu Ado Bayero Bayan nuna jimami da alhinin abunda ya faru ya yi addu’ar fatan samun lafiya a garesu da kiyayewar afkuwar hakan.

Sarkin yayi addu’ar Allah ya gafartawa wadanda suka rasu yasa aljanna madaukakiya ita ce makoma a garesu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *