Dan takarar majalissar tarayya a kananan hukumomin Wudi da Garko a jihar Kano , Barista Ahamd Sani Bawa, ya bukaci alúmmar jihar da kasa baki daya su fito su yi rijistar katin zabe don kada shugaban kasa mai ci Bola Ahmad Tinubu a zaben 2027.
Barista A. S. Bawa ya ce babu wanda yafi cancanta yan Nijeriya su zaba don ya zama shugaban kasa, sai Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar, saboda kwarewarsa da kuma jajircewa wajen iya jagorancin al’umma.
Lauyan ya bayyana hakan ne ya yin da yake ganawa manema labarai a jihar Kano.
- Yan Sanda Sun Kama Yan Fashin Da Suka Jiwa Matar Aure Rauni Ta Hanyar Cire Mata Hakori Mai Gwal A Kano
- Yan Sanda Sun Manta Hularsu A Motar Dalibi Bayan Karɓar Cin Hancin N99,000
Ya kara da cewa gwamnatin dake ci ta sanya miliyoyin yan Nijeriya cikin kangin talauci da yunwa da babu wanda zai ceto su daga wannan hali na kunci sai Alhaji Atiku Abubakar domin yasan dukkan matsalolin dake damunsu.
A karshe ya yi fatan yan Nijeriya za su farka daga bacci wajen zabin shugaba nagari irin Wazirin Adamawa wanda zai himdita musu bisa alkawarin da ya daukar musu idan sun zabe shi a shekarar 2027.