Mai POS Ya Samu Kyautar N500,000:00 Bayan Ya Mayar Da Kudin Da Aka Tura Masa Bisa Kuskure A Kano.

Spread the love

Wani matashi mai suna Muhammadu Sani Abdurraham, dake gudanar da sanar POS, a shatale-shatalen Baban Gwari Kano, ya mayar da kudi naira miliyan Tara da dubu dari tara da chasa’in da Tara, da aka tura masa bisa kuskure.

Tun a ranar 21 ga watan Disambar 2023, ne mai sana’ar POS , ya garzaya wajen jami’an yan sanda, tare da shaida mu su cewar wani Abokin kasuwancinsa , da bai San ko waye ba, ya tura masa Naira miliyan goma ( 10, 000:00) maimakon naira dubu Goma ( 10, 000) da zai tura masa, bisa kuskure amma yanzu Naira miliyan Tara da dubu Dari Tara da chasa’in da Tara ( N9, 990,000:00), suna wajen sa domin nemo mai kudin a bashi abunsa.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta cikin Wata sanarwa da ya aike wa da jaridar idongari.ng, a ranar Alhamis , ya ce bayan karbar korafin Kwamishinan yan sandan jahar Kano, CP Muhammed Usaini Gumel, ya bayar da umarni ga sashin binciken kwakwaf (CID) karkashin jagorancin SP Abdulwahab Zubairu , domin lalubo ainishin mai kudi don Mayar masa.

CP M.U. Gumel, Gwamna Abba K. Yusuf Sun Taya Murna Ga Yan Sandan Da Suka Samu Karin Girma A Kano.

SP Abdullahi Kiyawa, ya Kara da cewa a wannan rana ta Alhamis, bayan yin zurzurfan bincike, sun Kai ga gano mamallakin kudin, Wanda yake gudanar da harkokin kasuwancin sa a Kasuwar Hatsi ta Dawanau a jahar Kano.

Kwamishinan Yan Sandan Kano CP Muhammed Usaini Gumel, ya gode wa mai sanar’ar POS din bisa gaskiyar da ya nuna, har dawo da kudin da aka tura masa bisa kuskure.

Yanzu haka dai an dawo wa da Dan kasuwar kudin sa naira miliyan Tara da dubu Dari Tara da chasa’in ( N9,990,000) har ya bayyana jin dadin sa ga mai POS din, sannan ya bashi kyauatar Naira dubu dari biyar N500,000:00.

A karshe Dan kasuwar ya yaba wa Kwamishinan yan sandan jahar Kano, bisa gaskiya, karanci da yake nunawa Wanda ya zamo abun koyi.

Shima mai sana’ar POS , ya godewa Allah da aka samu mai kudin har aka mayar masa domin ya ce , tunda wancan lokacin ko baccin Kirki baya iya yi saboda damuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *