Mai shari’a Binta Nyako na babbar kotun tarayya da ke Abuja, wadda ita ce ke gudanar da shari’ar jagoran ƴan awaren Biyafara, Nnamdi Kadu ta janye daga shari’ar.
Ta janye ne a ranar Talata bayan Mista Kanu ya miƙa buƙatar hakan, domin a cewarsa ba shi da ƙwarin gwiwar samun adalci a wajen ta.
Tun a farko, Lauyan gwamnatin Najeriya, Adegboyega Awomolo ya bayyana wa kotun cewa akwai wani shaida da yake so ya gabatar, amma yana buƙatar a ba shi kariya, sannan ya ce a shirye yake a cigaba da sauraron ƙarar.
Sai dai lauyan Nnamdi Kanu Aloy Ejimako ya bayyana wa kotun cewa ba su shirya cigaba ba, inda ya ce ana hana wanda yake wakilta damar shiryawa domin kare kansa. Lauyan na cikin magana a gaban kotun ne, Nnamdi Kanu ya miƙe ya ce masa ya zauna.
Bayan haka ne mai shari’ar ta sanar da janyewarta daga shari’ar, sannan ta ce za ta miƙa takardun zuwa ga babban alƙalin kotun.