Maiduguri: Gidan Radio Ndarason International Ya Zargi Hukumomin Tsaro Da Kama Ma’aikatansa 9.

Spread the love

Kafar yaɗa labarai ta Radio Ndarason International ta ce jami’an tsaro a jihar Borno sun kama ma’aikatanta tara, ciki har da babban editanta.

Wata sanarwa da kafar ta fitar ta ce an kama su ne yayin da suke tsaka da gudanar da aikinsu na ba da rahoton yadda zanga-zangar matsin rayuwa ke gudana a jihar.

“Shugabannin RNI na neman a sako musu ma’aikatansu nan take kuma sun koka kan yadda jami’an tsaro ke yunƙurin tilasta wa ‘yanjarida game da aikinsu,” in ji sanarwar.

Sai dai wani bidiyo da kafar ta yaɗa a shafinta na X ya nuna wasu daga cikin ‘yanjaridar lokacin da suke fita daga wajen jami’an tsaron.

Tuni gwamnatin jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya ta saka dokar hana fita, yayin da wasu rahotonni ke cewa an kashe mutane yayin zanga-zangar.

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *