Majalisa ta yi karatu na biyu ga kudirin bai wa daliban Najeriya bashin karatu

Spread the love

Majalisar wakilan Najeriya ta yi karatu na biyu ga kudirin bai wa daliban kasar rancen kudi domin karatu.

Majalisar wadda ta yi hakan a zamanta na ranar Alhamis, ta ce kudirin na son samar da wata hukuma wadda za ta rinka bai wa dalibai rancen kudi domin karatun makarantun gaba da sakandare .

Kafin dai tattaunawa kan kudirin, sai da shugaban majalisar wakilan, Abbas Tajuddeen ya fara da karanta wasikar da shugaba Tinubu ya aikewa da majalisar da ke neman goyon bayan majalisar wajen tabbatar da inganta rayuwar daliban Najeriya.

Kafin nan dai shugabannin kungiyar daliban Najeriya sun fara kun far baki wajen neman dalilin da ya sa har yanzu ba a tabbatar da kudirin ba, inda suke kwatanta al’amarin da sun gaji da gafara sa ba su ga kaho ba.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya saka wa dokar bai wa daliban kasar na manyan makaratun da suka fito daga gidajen masu karamin karfi damar samun rancen karatu maras ruwa daga gidauniyar bayar da bashin karatu ta kasar.

Yan Sandan Kano Sun Gurfanar Da Mutumin Da Ya Makure Wuyansa Da Kebir Saboda tsananin Rayuwa

Hukumar kwastam a Sokoto da Zamfara ta saki motoci 15 na hatsi da aka kama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *