Majalisar jagororin addinai ta Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar ƙoli ta harkokin addinin musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’adu Abubakar III, da shugaban ƙungiyar kiristoci ta Najeriya (CAN). Archbishop Daniel Okoh ya yi kira da a gaggauta kawo ƙarshen zanga-zangar adawa da matsin rayuwa da ke gudana a faɗin Najeriya
Sun yi wannan kiran ne a yau Juma’a cikin wata sanarwa da suka sanyawa hannu tare da babban sakataren majalisar NIREC, Farfesa Cornelius Afebu Omonokhua.
“Majalisar NIREC ta lura da abubuwan da ke faruwa a ƙasar a halin yanzu. Zanga-zangar wanda aka faro cikin lumana a ranar Alhamis, 1 ga watan Agusta, 2024 ta ɗauki wani salo na tashin hankali daga baya.
Sanarwar ta ƙara da cewa “A cikin ƴan sa’o’i kaɗan an yi asarar rayuka da dukiyoyi sakamakon wannan mummunan yanayi.”
Majalisar ta amince da cewa ana fuskantar wahalhalu da dama a ƙasar amma ta ce tashin hankali ba shi ne mafita ba, inda ta ƙara da cewa hakan zai ƙara dagula halin da al’ummar ƙasar ke ciki.
“NIREC tana kira ga ƴan Najeriya da su janye wannan zanga-zangar su baiwa gwamnati damar wanke kanta.” In ji sanarwar
NIREC ta buƙaci gwamnati da ta gaggauta ɗaukar matakai domin biyan buƙatun ƴan ƙasar.