Majalisar Dattawan Najeriya ta ce ta kafa kwamitin gaggawa da zai gudanar da bincike kan kisan da aka yi wa sojojin ƙasar 17 a jihar Delta.
Majalisar ta bayyana hakan lokacin da aka gabatar da kudurin da yake neman a yi bincike kan kisan sojojin, tana cewa ba za ta zuba ido lamarin ya tafi a haka ba, don guje wa ɗauki matakin ramuwar gayya daga sojojin.
Sanata Muhammad Adamu Aleru, mamba a kwamitin sojin ƙasa na majalisar dattawan, ya bayyana wa BBC cewa abin da aikata wa sojojin yana da munin gaske.
“Mun nuna rashin daɗin mu kan abin da ya faru, wannan abin bai kamata ba kan mutanen da suka fito su are rayukan ƴan ƙasa,” in ji Aleru.
Ya ce ba wata ƙasa a duniya da za ta lamunci irin haka.
Sanata Aleru ya ce kwamitocin sojin ƙasa da sojin sama da kuma na ruwa za su tattauna da manyan hafsoshin tsaron ƙasar wajen ganin an zaƙulo waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki tare da hukunta su don haka ya zama darasi ga na baya.
Majalisar dattawan ta kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta biya diyya ga iyalan sojojin 17 da aka kashe.
Jami’an Yan Sandan Kano 63 Sun Sami Karin Girma Daga DSP Zuwa SP.
Kotu ta ƙi amincewa da belin Nnamdi Kanu