Majalisar dattawa ta yi sammacin manyan hafsoshin sojin Najeriya kan matsalar tsaro

Spread the love

Majalisar dattawa ta yi sammacin manyan hafsoshin tsaron Najeriya game da kalubalen tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a fadin kasar.

Yan majalisar sun yi wannan kira a karkashin murya guda bayan wani zaman gaggawa da suka yi bayan dawowarsu bakin aiki karon farko a wannan shekarar.

Majalisar dattawan ta yi zaman gaggawar ne bayan da shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar da kuduri a madadin sanatocin kan yanayin tsaro a Najeriya.

An bai wa iyalan ‘yan sandan da suka mutu naira miliyan 135 a Zamfara

Yar Najeriya ta soma bulaguro daga London zuwa Legas a mota

Bayan shafe kusan sa’a biyu suna taron sirri, majalisar ta sake haduwa tare da yanke shawarar gayyato manyan hafsoshin tsaro a mako mai zuwa game da karuwar rashin tsaro a kasar.

Manyan hafsoshin tsaron sun hada da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa da shugaban rundunar sojin kasa, Leftenant Taoreed Lagbaja da shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar da shugaban rundunar sojin ruwa Vice Admiral Emmanuel Ogalla.

Majalisar ta kuma dage zamanta zuwa 6 ga watan gobe na Fabarairu domin bai wa yan majalisar damar yin zabe a zaben cike gurbi na ranar Asabar.

A baya-bayan nan, an ga karuwar matsalar tsaro a Abuja, babban birnin kasar da jihar Filato da wasu sassan Najeriya da aka samu karuwar garkuwa da mutane don kudin fansa da kashe-kashe na baya-bayan nan shi ne kisan wasu sarakunan gargajiya da kuma sace daliban makaranta da malamai a jihar Ekiti.

Ko a jiya, tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya soki Shugaba Bola Tinubu da yin tafiye-tafiye yayin da kasar ke fama da matsalolin tsaro sai dai a martaninta, gwamnati ta ce tana yin duk mai yiwuwa domin dakile matsalar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *