Majalisar Dattawa ta Najeriya ta bayyana aniyarta ta gayyatar babban bankin ƙasar da sauran jiga-jigan da ke kula da harkokin man fetur game da zargin yi wa ɓangaren man zagon ƙasa.
Shugaban kwamatin wucin-gadi kan zargin lalata harkokin mai kuma shugaban masu rinjaye, Opeyemi Bamidele, ya ce kwamatin nasa zai binciki biliyoyin dala da aka kashe wajen gyaran matatun mai na ƙasar.
An tsara gudanar da zaman jin ra’ayin jama’a ranar 10 ga watan Satumba, inda ‘yankwangilar da ke aikin gyaran matatun za su hallara domin amsa tambayoyi.
Kazalika, kwamatin mai mambobi 14 zai ziyarci jihohin Legas da Rivers da kuma Bayelsa domin ganawa da masu ruwa da tsaki a fannin man fetur.
A jawaban da suka gabatar, ‘yan kwamatin sun ci alwashin yin aiki ba sani ba sabo domin daƙile matsalolin da ke addabar sashen shekara da shekaru.