Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da kudurin sauya dokar albashi mafi ƙanƙanta bayan shugaban ƙasa ya aika da buƙatar a yau Talata.
Majalisar ta mince da kuɗirin ne da ke neman tabbatar da ƙarin albashi mafi ƙanƙanta daga N30,000 zuwa N70,000 bayan tsallake karatu na biyu da na uku ba tare da ɓata lokaci ba.
A makon da ya gabata ne ƙungiyoyin ƙwadago suka amince da tayin N70,000 bayan tattaunawa da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Rahotanni sun ce kudirin da shugaban ya aika wa majalisam ya ƙunshi har da buƙatar neman sauya shekarun ƙarin albashi daga shekara biyar zuwa uku.