Majalisar dattijan Najeriya na so a bai wa ƙananan hukumomi ƴancin kai

Spread the love

Majalisar Dattijan Najeriya ta nemi Shugaba Tinubu ya shige gaba domin nema wa kananan hukumomi ‘yanci a wajen jihohi, wanda suka ce hakan zai iya magance matsalar tsaro da ake fama da ita da tururuwar da mutane ke yi zuwa birane da kuma rashin aikin yi.

Sanata Abdurrahaman Kawu Sumaila ne ya gabatar da kudurin wanda ya ce akwai bukatar a zauna da gwamnoni da masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a yi kananan hukumomi su samu ‘yancinsu da suka rasa a baya.

Kawu Sumaila ya ce a wannan lokacin za a samu nasara saboda salon da majalisar ta dauka a wannan karon ya sha banban da matakan da aka rika dauka a baya.

Sanatan ya ce sun nemi shugaban kas aya shige gaba wajen tabbatar da an samu abinda ake so, ta hanyar kiran taron masu ruwa da tsaki da zai kunshi gwamnoni da ýan majalisu na tarayya da na jihohi da shugabannin al’umma da malaman addini da sauransu domin a tattauna domin samarwa kananan hukumomi matsaya guda.

Kawu Sumaila ya ce idan har aka samu nasarar daukar matakin za a samu saukin rashin tsaro da talauci da ya addabi jihohin arewacin Najeriya, ” A cikin wata uku abubuwa za su canja, idan aka ce a karamar hukuma za a yi tasarrafin miliyan 300 ko miliyan 400, bayan an biya ma’aikata duk wasu kananan ayyuka za a yi.”

Sanata Kawu ya ce ba abin birgewa ba ne ace anyi zabe amman jam’iya guda za ta lashe zaben kananan hukumomi ” kai an zabe ka, yan majalisar jihohin ka daga jam’iyu daban-daban, amman ranar zaben kananan hukumomi jam’iya guda za ta lashe, kai kasan ba gaskiya ake yi ba. “

Mafi yawan tsofaffin shugabannin kananan hukumomin da BBC ta tattauna da su sun bayyana cewa wannan matsala ta fara ne a 2007 amma a wasu johohi kadan kafin daga bisani ta mamaye kasar baki daya.

Masu sharhi kan lamuran yau da kullum na ganin ba ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kai ne kawai zai iya kawo karshen matsalarsu a Najeriya saboda su ne suka fi kusa da jama’a kuma su suka fi sanin matsalolinsu ta yadda za su magance su.

Sai dai wasu na ganin su ma suna da nasu laifukan wadanda ke da alaka da zargin cin hanci da rashawa, ko da yake sun sha musantawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *