Kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Jibril Falgore tare da rakiyar wasu jagororin majalisar sun isa gidan gwamnati domin kai wa gwamna sabuwar dokar masarautu da majalisar ta yi wa kwaskwarima.
Dazu da safe ne majalisar ta yi wa dokar masarautun jihar ta shekara 2019 kwaskwarima, inda ta soke duka masarautun jihar biyar.
Wakilin BBC da ke Kano ya ce a halin da ake ciki gwamnan tare da ‘yan majalisar suna cin abincin rana ne a gidan gwamnati, inda ake sa ran gwamnan zai saka hannu kan sabuwar dokar da zarar sun kammala cin abincin.
Wasu majiyoyi a gidan gwamnatin sun shaida wa wakilin namu cewa tuni masu zaɓen sarki a Kano suka isa fadar gwamnatin jihar, wataƙila domin shirye-shiryen zaɓen sabon sarki.
- An kuɓutar da ‘ya’yan ɗan majalisar Zamfara bayan wata 17 da sace su
- Rushe Sarakuna: Radio Kano Ta Yi Mubayi’a Ga Matakin Majalisar Dokokin Jihar