Majalisar dokokin jihar Katsina ta buƙaci kamfanin sadarwa na MTN ya daina yawan katse sabis ba tare da yin gamsasshen bayani ga al’umma ba.
Majalisar ta bayyana cewa yawan katse sadarwar na cutar da kasuwanci da zamantakewar al’ummar jihar.
Cikin wani ƙudirin gaggawa da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dandume, Hon. Yahaya Nuhu Mahuta ya gabatar a zauren Majalisar ranar Talata, ya ce katse sabis da kamfanin ke yi ya shafi ɓangarori kasuwanci, ilimi da harkokin yau-da-kullum na al’ummar jihar.
Mataimakin kakakin majalisar jihar, Honarabul Hon Abduljalal Haruna Runka ya shaida wa BBC cewa haƙƙin kamfanin ne ya samar da nagartattun ayyuka, domin al’umma kuɗi suka biya don neman biyan buƙata.
Ya bayyana cewa babban takaicin, kamfanin bashi bada wani uzuri ko cikakken bayani akan dalilin ɗaukewar sabis ɗin.
Hon. Mahuta ya ce al’umma suna da hakki a kan kamfanin, kuma gazawar zai baiwa alummar damar chanza tsarin da suke ganin zai taimake su.
Haka kuma majalisar na duba yiwuwar gayyato kamfanin domin yin gamsasshen bayani ga majalisar kan dalilin yin haka.
- Soja Ya Sumar Da Wata Da Mari A Abuja
- An yanke wa malamin makaranta ɗaurin shekara 15 saboda yi wa ɗalibarsa fyaɗe
Mataimakin kakakin majalisar, ya umarci kwamitin sadarwa na majalisar ya aiwatar da bincike a kan koken, tare da kawo rahoto cikin mako biyu.