Majalisar Dokokin Neja Ta Nuna Damuwa Kan Yadda ‘Yanbindiga Suka Mamaye Dajin Horar Da Sojojin Najeriya

Spread the love

Majalisar Dokokin jihar Nejan Najeriya ta nuna damuwa tare da fargaba kan yadda ‘yanbindiga suka kwace babban dajin nan na horar da sojojin kasar da ke yankin karamar hukumar Kontagora.

A wani zama da Majalisar ta gudanar a ranar Talata Mamba a Majalisar Mai wakiltar Kontagora ta 2 Hon. Abdullahi Isah ya ce yanzu ‘yanbindiga sun kwacewa sojojin Najeriya wannan daji kuma anan ne suke kai mutanen da suka yi Garkuwa da su domin neman kudin fansa.

Majalisar Dokokin jihar Nejan dai ta bukaci Gwamnatin jihar da Hukumar Sojin kasar da su yi duk mai yiwuwa domin kwato wannan daji na horar da sojojin daga hannun ‘yanbindigar.

Hon. Sani Umar Blak Mamba ne a Majalisar Mai Wakiltar Kontagora ta daya ya kuma ce lamarin yana da matukar tayar da hankaki.

Shi ma shugaban Karamar Hukumar Kontagora Hon Shehu s. Pawa ya tabbatar da cewa yanzu ‘yanta’adda ne ke rike da wannan daji ba sojojin Najeriya ba.

Sai dai a lokacin da na tuntubi mai magana da yawun rundubar sojin Najeriya da ke Barikin sojojin na Kontagora Captain Iliya Bawa ya ce ba gaskiya ba ne bayanin cewa ‘yanta’adda sun mamaye wannan daji.

Captain Iliya Bawa wanda bai amince da in nadi muryarsa ba ya ce jami’ansu kullun suna kan sintiri a wannan daji kuma yanzu haka akwai daruruwan farar hula da ke noma a dajin sakamakon yawan sintirin da sojojin ke yi.

VOAHAUSA

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *