Majalisar dokokin Rivers za ta tantance waɗanda ake son naɗawa kwamishinoni

Spread the love

Yan majsalisar dokokin Rivers da ke biyayya ga gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, za su tantance mutane takwas da gwamnan ya aika sunayensu, domin naɗa su kwamishinoni.

A wata wasika da akawun majalisar, Dr. G, N Gillis-West, ya aika, a jiya Litinin ya gayyaci mutanen da su bayyana a zaurn majalisar a yau Talata, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Wasikar ta nuna cewa, majalisar karkashin jagorancin shugabanta na bangaren da ke biyayya ga gwamnan, Victor Oko-Jumbo, na sa ran tantance mutanen zuwa karfe goma na safe.

Wannan shi ne karo na biyu da bangaren majalisar da ke biyayya ga Fubara zai tantance mutanen da za a nada kwamishinoni tun bayan da majalisar ta rabu biyu – masu biyayya ga gwamna da kuma masu biyayya ga tsohon gwamnan jihar kuma ministan Abuja Nyesom Wike.

A makon da ya gabata ne majalisar bangaren masu biyayya ga Gwamna Fubara ta tantance tare da tabbatar da babban lauya Dagogo Iboroma (SAN) a matsayin sabon babban lauyan gwamnatin jihar kuma kwamishinan sharia, bayan da Farfesa Zaccaeus Adangor, (SAN), wanda ke biyayya ga Wike ya sauka daga wannan mukami, sakamakon sabanin da ya ya tsananta tsakanin gwamnan da tsohon mai gidansa na siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *