Majalisar harkokin shari’a ta Najeriya ta nemi a kori alƙalai kan ƙarya a shekarunsu

Spread the love

Majalisar kula da harkokin shari’a a Najeriya ta bayar da shawarar yi wa wasu manyan alƙalai biyu ritaya saboda laifin yin ƙarya a shekarunsu na haihuwa.

Cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, National Judicial Council (NJC) ta ce ta gano Alƙalin Alƙlai na jihar Imo T. E. Chukwuemeka Chikeka, da shugaban kotunan shari’ar Musulunci na jihar Yobe Babagana Mahdi sun aikata laifi.

Haka nan majalisar ta ɗauki mataki kan wasu alƙalan da suka haɗa da na yin gargaɗi, da hana su albashi, da kuma saka musu ido bisa laifuka daban-daban da suka aikata.

A cewar sanarwar, binciken NJC ya gano alƙalin alƙalan na Imo na da ranakun haihuwa biyu na 27 ga watan Oktoban 1956 da 27 ga Oktoban 1958, yayin da shi kuma shugaban kotunan shari’a na Yobe yake da kwanan wata har uku daban-daban.

Bisa wannan dalili ne majalisar ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Imo da ke kudancin Najeriya shawarar yi wa Mai Shari’a Chikeka ritayar dole tare da ƙwace albashin da ya karɓa tun daga ranar 21 ga watan Oktoban 2021.

Kazalika, majalisar ta bai wa gwamnatin jihar Yobe shawarar yi wa Mai Shari’a Babagana Mahadi ritaya ta tilas, wadda ya kamata ya yi tun shekara 12 da suka wuce, sannan kuma ya dawo da albashin da ya karɓa na tsawon waɗannan shekarun.

Duk da cewa an fara gudanar da binciken tun kafin shugabar majalisar kuma alƙaliyar alƙalai ta Najeriya Kekere-Ekun ta samu muƙamin, matakan sun yi daidai da alwashin da ta ɗauka na dawo kima da martabar ɓangaren shari’a a Najeriya.

Lamarin na zuwa ne yayin da ƙungiyoyi da ‘yan gwagwarmaya ke caccakar Ministan Abuja Nyesom Wike saboda bai wa wasu alƙalai 40 kyautar gidaje, abin da ya ce manufa ce ta gwamnatin Bola Tinubu yake aiwatarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *