Majalisar Kenya ta amince da dokar ƙara haraji

Spread the love

Yan majalisar dokokin ƙasar Kenya sun amince da dokar ƙara haraji mai cike da cecekuce, wadda kuma ta janyo zanga-zanga a faɗin ƙasar.

Kudirin ya samu gagarumin rinjaye a lokacin karatu na biyu.

Shugaban majalisar ya ce a yanzu kudirin zai tsallake zuwa mataki na gaba inda wani kwamiti zai duba gyare-gyaren da suka shafi harajin da ake son ƙarawa.

Za a gabatar da kudirin dokar a ranar Talata mai zuwa. Masu zanga-zangar sun yi tir da ƙarin harajin tare da yin kira ga ‘yan majalisar da su yi fatali da kudirin wanda suka ce idan aka amince da shi zai yi illa ga tattalin arzikin ƙasar da kuma janyo tsadar rayuwa ga ‘yan ƙasar ta Kenya da ke fafutukar ganin sun samu rayuwa mai inganci.

Gwamnatin da ke fama da matsalar kuɗi, na neman tara sama da dala biliyan biyu domin gudanar da kasafin kudi da kuma rage basussukan da ake bin ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *