Majalisar matasan Arewa ta ce ta yi mamakin yadda kungiyar Arewa Consultative forum ta ce ta dakatar da shugabanta Mamman Mike Osuman saboda ya kalubalanci salon yadda Shugaba Tinubu ya yake mulkin Nigeriya.
” Babu shakka manufofin shugaban ƙasa Bola Tinubu suna Cutar da Arewacin Nigeria, don haka dole mu ga wani abun aibu ba don wani ya kalubalance su har ace za a dakatar da shi daga kan mukaminsa”.
Majalisar matasan Arewan ta bukaci kwamitin amintattun kungiyar ta ACF da ya gaggauta janye dakatarwar da ya yiwa shugaban kungiyar ko su dauki matakan da suka dace.
Majalisar matasan Arewa ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta aikowa kadaura24, mai dauke da sa hannun akalla mutane 21.
Matakin da kungiyar ACF ya dauka bai dace ba kuma Muna Allah-wadai da shi, bai kamata ace kwamitin amintattun kungiyar ya shiga al’amarin kungiyar na yau da kullum ba, ko da yake ba mu yi mamaki kasancewar tun kafauwar kungiyar AFC sama da Shekaru 24 ba wani abun a zo a gani da kungiyar ta tsinanawa yan Arewacin Nigeria”. A cewar sanarwar.
Sanarwar ta kara da cewa matukar kwamitin amintattun kungiyar ACF suka kasa daukar matakin da ya dace na janye dakatarwar da suka yiwa shugabannasu, za su fara hada kan matasan Arewacin Nigeria domin marawa duk wani dan arewa baya a zaben shugaban ƙasa na 2027 dake tafe.