Majalisar wakilan Najeiya ta bayyana shirin gudanar da bincike kan zargin da ake yi na cewa man fetur da ake samu daga matatar Dangote bai kai kyawun da ingancin wanda ake shigowa da shi daga ƙasashen ƙetare ba.
Shugaban Majalisar Wakila, Tajudeen Abbas ne ya sanar da hakan a ziyarar da mamabobin majalisar suka kai matatar Dangote a ranar Asabar, inda ya nuna damuwar sa kan cece-ku-cen da ake tafkawa dangane da ingancin man da ake shigowa da shi Najeriya.
Aliko Dangote, shugaban kamfanin Dangote dai ya tabbatar da cewa kayan man fetur da matatarsa ke sarrafawa ingantattu ne kuma sun cika ka’idojin ƙasashen duniya.
Majalisar ta ce tana shirin kafa wani kwamiti da zai yi cikakken bincike da kuma gwada kayan da aka samu daga matatar ta Dangote da kuma sauran wurare.