Majalisar wakilai za ta binciki yawan lalacewar babban layin wutar Najeriya

Spread the love

Majalisar wakilan Najeriya ta umarci kwamitinta kan wutar lantarki da ya binciki dalilin da ya sa babban layin wutar lantarkin ƙasar ke yawan samun matsala, al’amarin da ke janyo katsewar lantarki a sasan ƙasar da dama musamman arewacin Najeriya.

Majlisar ta nemi kwamitin ya gabatar da rahoto nan da makonni uku masu zuwa.

Hon Mansur Manu Soro da ke wakiltar mazabar Darazo da Ganjuwa a jihar Bauchi a majalisar wakilan Najeriya, shi ne ya gabatar da kudurin.

Babban layin wutar na Najeriya dai ya lalace fiye da sau 10 a wannan watan inda a ranar ɗaya ma ya lalace sau biyu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *