Majalisar Wakilai za ta yi bincike kan batun sojan ruwa Seaman Abbas

Spread the love

Kwamitin sojin ruwa na majalisar wakilan Najeriya ya ce zai yi bincike dangane da tsare sojan ruwan nan Seaman Abbas Haruna na tsawon shekaru shida ba “bisa ƙa’ida” ba.

Wata sanarwa da shugaban kwamitin, Yusuf Adamu Gagdi ya wallafa a shafinsa na X, ta ce “an tsare Seaman Abbas Haruna ne bisa umarnin wani babban soja Birgediya Janar M.S Adamu. Saboda haka kwamitin zai bincika domin tabbatar da cewa duk waɗanda ke da hannu a al’amarin sun fuskanci hukunci daidai abin da suka aikata.”

Yusuf Gagdi ya ƙara da cewa “rashin imanin da aka nuna a kan sojan ruwan saboda ɗan saɓanin da aka samu tsakaninsa da babbansa ya sa mutane da dama sun zubar da hawaye a lokacin da mai ɗakinsa ke bayar da bahasin yadda a al’amarin ya faru a gidan rediyo da talbijin na Brekete.”

Da ma dai hedikwatar tsaron Najeriya ma ta ce ta ga wani bidiyo da ke yawo na zargin tsare wani sojan ruwa mai suna Seaman Abbas Haruna tsawon shekaru shida kuma tana bincike a kai.

Hedikwatar rundunar tsaron ta Najeriya a wata sanarwa mai sa hannun kakainta, Birgediya Janar Tukur Gusau ta “muna bai wa al’ummar Najeriya tabbacin cewa rundunar tsaron Najeriya a shirye take ta samar da adalci da daidaito bisa dokokin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *