Majalisar wakilan Najeriya ta ba da shawarar gina gidajen yari na zamani

Spread the love

Majalisar wakilan Najeriya ta bayar da shawarar a gina gidajen yari na zamani a jihohin 36 na ƙasar domin kaucewa yawan fasa gidajen da ake fama da shi.

Shugaban kwamitin gidajen gyaranChinedu Ogah ne ya bukaci hakan yayin da kwamitin ya kai ziyara gidan yarin Suleja da aka fasa kwanakin baya.

Ya ce akwai bukatar a samarwa fursunonin tsari mai kyau na wajen zama, “dan abin da ake ciyar da su baya isa, muna da bukatar kula da gidajen yarinmu yadda ya kamata”.

“Garambawul din da aka yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya mayar d gidajen yari zuwa karkashin kasafin kudi na yau da gobe; dan haka dole duka gwamnatin jihohi 36 da muke da su su yi aiki da doka wajen gida sabbin gidajen yari na zamani.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *