Majalisar wakilan Najeriya ta jingine ƙudurin ‘ɗaure masu zanga-zanga ba bisa ƙa’ida ba’

Spread the love

Shugaban Majalisar Dokokin Najeriya, Tajudeen Abbas ya sanar da janye ƙudurin da ya gabatar na samar da dokar ‘hukunta masu ayyukan tayar da hargitsi da waɗanda suka ƙi rera taken ƙasa’, wanda ya gabatar a zauren majalisar.

Wannan matakin na zuwa ne bayan lamarin ya janyo ce-ce-ku-ce da suka mai zafi tsakanin ƴan Najeriya, musamman matasa.

Matasan sun yi zargin cewa ana ƙoƙarin ɓullo da dokar ne domin murƙushe duk wani yunƙuri na yin zanga-zanga, bayan zanga-zangar matsin rayuwa da al’ummar ƙasar suka gudanar a farkon wannan wata na Agusta.

Shugaban Majalisar wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas ne ya gabatar da dokar, mai taken ‘Counter Subversion Bill 2024’ a ranar 23 ga watan Yuli, inda ƙudurin ya tanadi hukunce-hukunce ga mutanen da aka kama da laifin zagon ƙasa ko tayar da hankali ko alaƙa da wasu ƙungiyoyin da aka haramta.

Wani ɓangare na dokar ya tanadi cewa: ‘Duk mutumin da aka kama da laifin yin karan-tsaye ga zirga-zirgar ababen hawa, ko datse hanya ko ƙaƙaba dokar zaman gida, ko yin tattaki ba bisa ƙa’ida ba ko kuma wasu abubuwa masu kamanceceniya da hakan zai fuskanci tarar naira miliyan biyu ko kuma ɗaurin shekara biyar a gidan yari.’

Haka nan wani ɓangare na ƙudurin dokar da ya ja hankalin al’umma shi ne wanda ya ce: ‘Duk wani mutum da ya lalata wani tambari na ƙasa, ko ya ƙi rera taken ƙasa, ko ya yi ƙoƙarin lalata wurin ibada da nufin haifar da rikici da yi wa gwamnati ɓarna, ya aikata laifi wanda za a buƙace shi ya biya tarar naira miliyan biyar ko zaman gidan yari na shekara 10.’

A cikin sanarwar janye ƙudurin dokar, wadda ta samu sa hannun mai taimaka wa shugaban Majalisar wakilan kan yaɗa labarai, Musa Abdullahi Krishi, ta ce an janye dokar ne “bayan tattaunawa mai zurfi da masu ruwa da tsaki da kuma kyakkyawan la’akari da halin da ƙasa ke ciki.”

Sanarwar ta ƙara da cewa Honorabul Abbas “ba zai taɓa goyon bayan duk wani mataki da zai yi illa ga zaman lafiya da haɗin kan al’ummar ƙasar ba.”

Zanga-zangar da wasu ƴan ƙasar suka gudanar a cikin wannan wata na Agusta ya rikiɗe zuwa rikici a wasu jihohin ƙasar.

Yunƙurin da hukumomi suka yi na killace masu zanga-zanga a wani keɓeɓɓen wuri a biranen Abuja da Legas ya janyo taƙaddama tsakanin masu zanga-zangar da jami’an tsaro.

Haka nan hatsaniyar da ta faru, bayan mutane sun tare hanyoyi a da yin tattaki a wasu birane kamar Kano da Kaduna sun haifar da taƙaddamar da ake zargin ta janyo asarar rayuka da dukiya mai yawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *