Majalisar Wakilan Najeriya ta sanya wa’adin kammala gyaran tsarin mulkin kasar

Spread the love

Majalisar wakilan Najeriya ta karbi kudurin sake nazari da kuma gyara a kundin tsarin mulkin kasar har guda 40, kamar yadda mataimakin shugaban majalisar Benjamin Kalu, ya bayyana.

Mista Kalu ya kuma majalisar na duba yuwuwar sanya wa’adin zuwa watan Disamba na 2025 domin kammala gyaran fuskar.

Kalu, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin gyara kundin tsarin mulkin yana bayani ne ga manema labarai a yayin taron farko na kwamitin a Abuja.

Dan majalisar ya ce suna dubawa ne su yi nazari domin ganin kwamitin ya kammala aikin a lokacin da ba zai ci karo da harkokin zabe ba, musamman ma watan Disamba na 2025.

Ya ce tun 2010 majalisun dokokin kasa sun yi nasarar yin muhimman sauye-sauye a kundin tsarin mulkin bayan da gwamnatin mulkin soja ta Janar Abdulsalam Abubakar ta samar da shi.

An kama masu garkuwa da mutane 5, a Dajin Ivu dake Imo

Sauye-sauyen da suka hada da na bangaren shari’a da harkokin zabe da rage shekaru da bayar da damar nada matasa a shugabancin hukumar zabe, INEC ko kuma kwamishinoninta na jiha, da kuma bayar da gama ga matasa su yi takarar wasu mukamai.

Kwamitin mai mutum 37 ya kunshi wakilai daga jihohi 36 da kuma babban birnin tarayyar kasar Abuja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *