Kakakin majalisar wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas ya ce majalisar za ta ƙarfafa dokar ɓata-suna da cin cin mutuncin mutane da kuma cin zarafin mutane ta intanet.
Honarabul Tajedeen ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai kan abubuwan da ke damun ƙasar da aka gudanar a wani ɗakin taro a harabar majalisar.
Kakakin majalisar ya ce manufar dokar ba zai ci karo da ‘yancin faɗar albarkacin baki, amma za ta kare mutane da hukumomi daga cin zarafinsu a intanet.
An fara taron ministocin harkokin wajen ƙasashen Ecowas
Hukumar yaƙi da rashawa ta Kano za ta fara binciken masu ɓoye kayan abinci
Ya ƙara da cewa dole ne ‘yan Najeriya su damu bisa yadda ake yawan cin zarafin jami’an gwamnati a shafukan intanet.
Honarabul Abbas ya bayyana yadda kakakin majalisar da ya gabace shi, Femi Gbajabiamila, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fuskanci cin zarafi da intanet, da ɓata suna.