Majalisar zartarwar Najeriya za ta tafi hutu

Spread the love

Majalisar zartarwar Najeriya ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar, Bola Tinubu ta sanar da cewa za ta tafi hutu daga ranar 18 ga watan Disamban 2024 zuwa 6 ga watan Janairun 2025.

Majalisar ta bayyana hakan ne bayan wata tattaunawa da ta gudanar yau Litinin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

A bayanin bayan taron majalisar, hakan na nufin ba za a gudanar da wani taron majalisar ba a tsawon lokacin da za ta kwashe tana hutu.

Majalisar zartaswar Najeriya ta ƙunshi shugaban ƙasa da mataimakinsa da kuma ministoci.

Sanarwar da majalisar ta fitar ta nuna cewa a taron na yau Litinin ta kuma tattauna batun kasafin kuɗin shekarar 2025, da shugaban ƙasar zai gabatar a zauren Majalisar dokokin ƙasar.

Sufuri kyauta:

Majalisar zartaswar ta kuma ayyana sufuri kyauta ga ƴan ƙasar daga ranar 20 ga watan Disamba, 2024 zuwa 5 ga watan Janairun 2025 zuwa sassa daban-daban na ƙasar, kamar yadda gwamnati ta saba yi a lokacin “bukukuwan Sallah da na Kirisimeti.”

Sauya sunan jami’ar Abuja:

“Majalisar ta kuma amince da sauya sunan Jami’ar Abuja zuwa sunan tsohon shugaban ƙasar mulkin soji, Janar Yakubu Gowon, matakin da majalisar ta ce za ta gabatar gaban majalisar dokokin ƙasar domin neman amincewa.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *