Majalissar dokokin jahar Kano ta bukaci gwamnan jahar Engr. Abba Kabir Yusuf , da ya umarci hukumar tsaro ta farin kaya DSS da rundunar yan sandan Kano da su sanya ido kan Malamin nan Baffa Hotoro, tare da gurfanar da shi a gaban Majalissar Malamai da hukumar Hisbah reshen jahar ,bisa wasu munanan kalamai da ya furta kan mutanen garin Tudun Biri a jahar Kaduna.
Dan majalissar dokokin jahar Mai wakiltar karamar hukumar Kiru Hon. Usman Abubakar Tasi’u , ne ya gabatar da kudirin gaggawa a zauren majalissar kuma ta amimce da shi.
Usman Tasi’u ya ce , kalaman batancin da malamin ya yi kan mutanen Tudun Biri a karamar hukumar Igabi ta jahar Kaduna, za su iya haifar da riciki , kan hakan ne ya ja hankalin majalissar ta dauki matakin da ya dace dan yi wa tufkar hanci.
Tuni dai majalissar ta yi kira ga gwamnantin Kanon ta dauki mataki akan Malamin.
“Wadannan kalamai da ya yi kalamai ne ma su muni, abu ya faru na hatsari na Bomb wanda sojojin Nijeriya suka jefa ga wasu mutane da suke gudanar da addu’o’in Maulidi da ya yi sanadiyar mutuwar rayuka da yawa , wasu kuma suna can a Asibitoci a kwance”cewar Hon.Usman Tasi’u”.
Ya kara da cewa , bai yiwu wa mutanen da duka musulimi da wadanda ba musulmi ba , duk sun bayyana alhinin su kan faruwar wannan abu , amma ace wani mutum dan cikin jahar Kano wanda jahar Kano ta yi nisa a harkar addinin musulinci ba wai a Nijeriya ba , a Afrika ita ce jaha ta farko wacce ta ke jaha ta musulinci ace wai dan ta ya foto ya na wasu kalamai wanda kalaman ya saba wa shari’ar musulinci da addinin mu .
Anga Baffa Hotoro a wani faifan vedio da ya ke yawo a shafukan sada zumunta tare da bayyana kausasan kalamai marasa dadin jin kan wadanda suka rasa rayukan su a wajen taron Maulidin garin Tudun Biri a jahar Kaduna.
Tuni al’umma da dama suka fara mayar wa da Baffa Hotoron martani musamman a shafukan sada zumun ta.
A watan Mayun 2023 ma dai anga Baffa Hotoro a wani faifan vedio yana neman afuwa kan cin zarafin Sheikh Dahiru Bauchi da yayi bayan da DSS suka kama shi.