Iyayen dalibin nan mai suna, Isah Umar , dake karatu a jami’ar Ahmadu Bello Zaria Kaduna , sun yi kira ga mahukunta da su sanya baki a sakar mu ,su dansu da ya shafe shekaru tara a hannun hukumar tsaron farin kaya ta kasa DSS.
An kama matashin dalibin ne tun a ranar 26 ga watan Nuwamban 2014, a jahar Kano cikin dare , da yanzu haka iyayen matashin suka bayyana cewa ba su san dalilin kama shi ba.
Isah Umar dan asalin karamar hukumar Ungoggo ne ta jahar Kano , wanda yake shekara ta biyu a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria kafin a kama shi.
Mahaifin dalibin Mallam Umar Suda, ya bayyana cewa, yanzu haka matarsa har matsala,ta samu saboda damuwa.
Sai dai ya ce bai san laifin da dan nasa, ya aikata ba, domin ko ganinsa ma basa iya yi, don dan uwansa ya yi iya bakin kokarinsa a fadin Nijeriya domin ganin an saki Isah Umar amma abun ya ci tura.
Hajiya Safiya Umar, ita ce mahaifiyar dalibin ta bayyana irin fargabar da ta ke ciki wanda ya haifar mata da lalurar gani saboda damuwa da ta tsinci kanta a ciki.
Yanzu haka dan majalissa mai wakiltar mazabar Wudil da Garko a majalissar dokokin Nijeriya Abdulhakim Kamilu Ado, ya bukaci majalisar dokakin kasa ta snaya baki domin a saki matashi kan shafe tsawon shekaru ba tare da sanin laifin da ya aikata ba.
Dan majalissar ya ce zai yi duk mai yiwu wa wajen ganin Hukumar tsaron DSS ta saki Isah Umar , dake karatu a jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria.
A shekarar 2017 wata kotu ta bayar da umarnin a saki matashin, amma har wannan lokaci bai shaki iskar yanci ba.
Kawo yanzu hukumar tsaron farin kaya DSS bata ce komai ba kan wannan lamari.