Makarantu a jihohi 14 na Najeriya na cikin haɗarin satar ɗalibai

Spread the love

Gwamnatin Najeriya ta gano wasu makarantu a jihohi aƙalla 14 da kuma birnin Abuja, da ke da raunin da za a iya kai musu hari, yayin da ake samun ƙaruwar satar ɗalibai a ƙasar.

Hajiya Halima Iliya, shugabar shirin samar da kuɗaɗen bayar da kariya ga makarantu na ƙasa, ta ce hukumar ta tattara bayanai da za su taimaka wajen kai wa makarantun ɗauki.

An ga watan azumin Ramadan a Najeriya

Abdulsalami ya nemi Nijar, Mali, Burkina Faso su koma ECOWAS

A shekarar 2014 ne aka kafa hukumar bayan sace ɗaruruwan ɗaliban makarantar Chibok da ke jihar Borno a arewa-maso-gabashin ƙasar.

Jihohin da wasu makarantunsu ke cikin haɗarin sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Borno, Benue, Yobe, Katsina, Kebbi, Sokoto, Filato, Zamfara da birinin Abuja. A cewar hukumar.

A ranar Alhamis da ya wuce ne ƴanbindiga suka sace ɗalibai 270 na makarantun firamare da sakandire a ƙauyen Kuriga da ke jihar Kaduna.

Haka kuma a ranar Asabar da ta wuce ne wasu ƴanbindigar suka sace ɗaliban makarantar tsangaya kimanin 15 a ƙaramar hukumar Gada a jihar Sokoto.

Sace-sacen sun biyo bayan sace wasu ɗaruruwan ƴangudun hijira a Ngala da ke jihar Borno da ake zargin ƴanBoko Haram da aikatawa.

Iyaye da ƴan’uwan ɗalibai da sauran waɗanda aka sacen na ci-gaba da roƙon gwamnati ta kuɓutar da su.

BBCH

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *