Fitacciyar ‘yar gwagwarmayar Ilimi kuma wadda ta taɓa lashe kyautar Nobel, Malala Yousafzai, ‘yar asalin Pakistan, za ta ziyarci ƙasarta ta haihuwa a karon farko cikin shekaru.
Matashiyar mai shekara 27 za ta halarci wani taro na kwana biyu – da zai mayar da hankali kan ilimin yara mata a ƙasashen musulmi.
An fitar da Malala Yousafzai daga Pakistan a shekarar 2012 bayan da wani ɗan ƙasar na ƙungiyar Taliban ya harbe ta a ka lokacin da take cikin motar ɗaukar ɗalibai.
Tun daga lokacin sau ƙalilan ta ziyarci ƙasar.
An gayyaci shugabannin Afghanistan waɗanda ‘yan Taliban ne – da ke taƙaita wa mata neman ilimi – zuwa taron, kodayake ba su ce komai ba game da gayyatar.