Malaman Kano sun sasanta Abba Kabir da Sheikh Daurawa

Spread the love

Gamayyar malaman addinin Musulunci ta jihar Kano ta ce ta sasanta gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf da Kwamandan Hisbah na jihar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa bayan rashin jituwar da ta kai ga ajiye aikin shugaban na Hisbah.

Bayan wata ganawa da ta gudana a daren ranar Litinin a gidan gwamnatin jihar ta Kano, sakataren Gamayyar malaman, Dakta Sa’id Ahmed Dukawa, ya bayyana cewa sun shiga tsakani ne sanadiyyar kiraye-kiraye daga ciki da wajen jihar na ganin an warware matsalar.

A cewarsa, matsayar da aka cimma na nufin cewa a yanzu babu batun murabus din Sheikh Daurawa daga shugabancin Hisbah.

Dukawa ya ce: “Ya (Daurawa) dawo aiki, zai ci gaba da aikinsa”.

A ranar Juma’ar makon da ya gabata ne Sheikh Aminu Daurawa ya sanar da saukar sa daga kan muƙamin na shugaban Hisbah.

Za mu tsaurara tsaro a rumbunan ajiye kayan abinci – NEMA

Najeriya da Qatar sun cimma yarjejeniyoyin hadin gwiwa

Daurawa ya ce ya yi hakan ne bayan kalamai na kashe ƙwarin gwiwa daga gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.

Kwana ɗaya kafin nan, gwamna Abba Kabir ya bayyana rashin gamsuwa game da salon wasu ayyukan hukumar ta Hisbah, inda ya kushe matakin da jami’an hukumar ke ɗauka na tursasa wa waɗanda ake zargi da ayyukan ‘rashin ɗa’a’ shiga motar sintiri.

Lamarin ya janyo zazzafar muhawara a ciki da wajen jihar, inda wasu ke ganin cewa kalaman gwamnan tamkar watsa wa kwamandan Hisban ƙasa a ido ne.

Sai dai makusantan gwamnan sun kare shi, tare da cewa an yi wa kalaman nasa mummunar fassara.

Wannan ne karo na biyu da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa zai sake komawa kan kujerar ta shugabancin Hisbah bayan yin murabus don ƙashin kansa.

Malamin ya taɓa yin murabus a lokacin tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje bayan saɓanin da ya samo asali daga bambancin ra’ayi mai nasaba da siyasa.

Sai kuma wannan karo inda ya sauka sanadiyyar rashin jin daɗi da gwamnan jihar ya nuna kan wasu matakan da yake ɗauka wurin yaƙi da ayyukan matasa waɗanda ke yaɗa ɗabi’u da suka saɓa wa addinin Musulunci a fili da kuma a shafin tiktok.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *