Hukumar Alhazai ta Najeriya, ta ce aƙalla maniyyatan Najeriya 51,447 ne za su sauke farali a aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.
Shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Juma’a a Abuja.
Arabi ya ce hukumar na tsare-tsare wajen ganin ta gudanar da aikin Hajji cikin nasara, ko da kuwa za a fuskanci kalubale.
Ya nanata cewa mMsulman Najeriya za su yi aikin Hajjin 2024 a adadin da babu wanda ya taɓa tunanin.
- Saliyo ta ayyana dokar ta-ɓaci kan maganin ‘Kush’
- Ana Zargin Kungiyar AOJF Da Siyar Da Shinkafar Da Fatima Dangote Ta Basu Don Rage Radadin Rayuwa.
“Shirye-shiryen Hajjin bana na ɗaya daga cikin mafi wahala da aka taɓa gani,” in ji shi.
Ya ce a baya, an samu lokaci mai yawa na yin shirin da ya kamata, amma a wannan karon, ƙasar Saudiyya ta ba su lokacin da ya kamata su kammala komai.
Malam Arabi ya ce gwamnatin tarayya ta shiga taimaka ta hanyoyi da dama, musamman ma ɓullo da wasu tsare-tsare na tallafa wa hukumar domin tabbatar da cewa al’amura su tafi yadda ya dace.
Ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta ware wa Najeriya kujeru 95,000 domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024.
- Sojojin sun yi wa ‘yan bindiga kwantan ɓauna, sun kashe uku a Kaduna
- Kotu ta nemi ƴansandan New York su biya matan da suka tilasta wa tuɓe hijabi diyyar $17.5