Maniyyatan Najeriya Na Cikin Rashin Tabbas Saboda Yajin Aiki

Spread the love

Jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya ta shiga rudani bayan kungiyoyin kwadagon kasar sun tsunduma yajin aiki a safiyar Litinin

Ma’aikatan sufurin jiragen sama sun Fara yajin aikin ne a yayin da ya rage mako guda a kammala da jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Kasa Mai Tsarki.

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta bayyana 10 ga watan Yuni 2024 a matsayin ranar da za ta kammala jigilar maniyyatan kasar domin sauke farali.

Tun a daren Lahadi kungiyoyin ma’aikatan sufurin jiragen sama suka umarci mambobinsu su dakatar da aiki daga karfe 12 na dare a fadin Najeriya.

Kungiyoyin manya da kananan ma’aikata, injiniyoyi, matuka jirage da ma’aikatan jigila da sauransu sun ba da umarnin ne bayan wani taron gaggawa da suka gudanar.

Sanarwar hadin gwiwar da suka fitar dauke da sa hannun Kwamared Ocheme Aba, (NUATE); Frances Akinjole, (ATSSSAN); Abdul Rasaq Saidu, (ANAP) da kuma Olayinka Abioye (NAAPE) ta umarci daukan rassan kungiyoyin su bi umarninn fara yajin aikin 100%.

Hakan na zuwa ne duk da cewa sanya bakin da jagororin majalisar dokoki ta kasa domin janye yakin aikin bai yi nasara ba.

Majalisar ta kira zaman ne domin lallashin shugabannin kungiyar kwadago na NLC da TUC su amince da tattaunawa da bangaren gwamnati kan dambarwar mafi karancin albashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *