Wasu manoma a Ƙaramar Hukumar Ɗanja sun nemi gwamnatin Jiihar Katsina da ta biya su diyyar gonakinsu da ta karɓa tsawon shekara biyar.
Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa Mai magana da yawun manoman, Shugaba Ɗan’azumi ya faɗi haka a lokacin da yake miƙa takardar koke ga wakilin Sarkin Kudun Katsina hakimin Ɗanja.
Manoman da wakilin hakimin Sarkin Fulani Ɗanja Alhaji Yazid Sadiƙ, wakilin manoman ya ce Naira miliyan goma ne adadin kuɗin da gwamnati za ta basu amma har yanzu shiru.
Shugaba Ɗan’azumi ya bayyana cewa sun miƙa kokensu ga ƙaramar hukumar Ɗanja da gwamnatin jiha da ɗan majalisar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar amma shiru kake ji kamar yaddaya faɗa wa wakilin hakimin halin ƙuncin rayuwa da suka shiga sanadiyyar rashin biyan wannan diyya.
- Musa Iliyasu Kwankwaso ya kama aiki a mukamin da Tinubu ya bashi
- Shugabannin duniya sun taya Pezeshkian murnar lashe zaɓen Iran
“Da noma muka dogara ga shi an amshe da niyyar biyarmu diyya yau shekara biyar kenan babu wani bayani,” ya ce. Shugaba Ɗan’azumi ya ƙara da cewa mutum 12 lamarin ya shafa da yanzu haka sun koma a gonakin wasu suke leburanci.
Sai ya roƙi hakimin da ta sa baki ko gwamnatin Dikko Raɗɗa ta biya su.
Shi ma Mataimakin Shugaban masu noman tumatir na asa Alhaji Hamisu Malam ya bi sahun kiraye-kiraye na neman gwamna Dikko Raɗɗa ya sa baki a biya su.
Ya ce yau shekara huɗu kenan da karban gonakinsu da niyar biyan su naira miliyan goma bayan an tantance gonakin tasu amma shiru.Da yake maida jawabi wakilin hakimin Sarkin Fulani Ɗanja ya nuna jin daɗinsu da yadda har suka yi haƙuri aka ɗauki tsawon lokacin. Ya yi alƙawarin gabatar da takardar kokensu ga hakimi da kuma tuntuɓar hukumomin da abin ya shafa.
- Gwamnatin Najeriya za ta maka Daily Trust a kotu
- SAVE OUR SOCIETY BY SIGNING THIS PETITION SEEKING TO STOP PRESIDENT TINUBU FROM LEGALIZING LGBTQ IN NIGERIA 2024