Manufofin Tinubu sun jefa ’yan Najeriya cikin ƙangin talauci — APC

Spread the love

Jam’iyyar APC mai mulki, ta amince da cewa manufofin Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun ƙara jefa al’ummar ƙasar nan cikin ƙangin talauci.

Sakataren Yaɗa Labaran Jam’iyyar APC na, Barrister Felix Morka ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja.

Ya bayyana haka ne yayin da yake yi wa tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na ƙasa (Arewa maso Yamma), Salihu Mohammed Lukman martani.

Lukman, ya zargi APC da gaza cika alƙawuran da ta ɗaukar wa ’yan Najeriya, inda ya ce tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba su cika alƙawuran yaƙin neman zaɓensu ba.

Ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyun adawa su haɗa kai su yi ƙoƙari wajen kawar da gwamnatin APC a zaɓen 2027.

Amma yayin da yake martani, Morka, ya ce Shugaba Tinubu yana ɗaukar matakan gyara domin farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar nan da ya daɗe da lalacewa.

Sai dai ya ce gyaran da ake yi ya ƙara jefa al’umma cikin wahalhalun rayuwa.

A cewarsa, “Gwamnatin APC ƙarƙashin shugabancin Shugaba Tinubu tana ɗaukar ƙwararan matakai domin gyara tattalin arziƙin ƙasar nan, inganta tsaro, da kuma kawo ci gaba mai ɗorewa.”

Ya ƙara da cewa rashin ɗaukar irin waɗannan matakai a gwamnatocin baya ne, ya jefa tattalin arziƙin ƙasar nan cikin mawuyacin hali na tsawon lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *