Manyan ɓarayi ma ba za su tsira ba a hannunmu – EFCC

Spread the love

Shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ya tabbatar da cewa ba za su bar manyan ɓarayi ba a yaƙin da suke yi da masu alaƙa da cin hanci da rashawa a ƙasar.

Mista Ola Olukoyede ya ce ba za su bar kowa ba a aikin da suke yi. Ya ce a daidai lokacin da suke bin manyan ɓarayi, za kuma su ci gaba da bin sawun ƙananan ɓarayi.

Ya ce aikin da EFCC take yi zai ci gaba da karaɗe ko’ina, da kuma kan kowa da kowa ba tare da wani da ke alaƙa da duk wani nau’in laifin kuɗi ko na tattalin arziƙi ya kuɓuta ba.

Shugaban na EFCC ya ba da wannan tabbaci ne ranar Lahadi lokacin da hukumarsa ta shirya wani taron wayar da kai da kuma yunƙurin shigar da jama’a cikin harkokin yaƙi da cin hanci da rashawa.

A cewarsa, a cikin wata biyun da ya wuce, hukumarsa ta EFCC ta gurfanar da tsoffin gwamnoni guda biyu gaban shari’a.

Ana dai sukar hukumar ta EFCC da cewa ta zama kyanwar lami, ba ta iya bin manyan ‘yan siyasa da sauran manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati waɗanda ake zargi da tafka gagarumar sata da kuma almundahana da dukiyar al’umma.

Sai dai, Mista Ola Olukoyede ya ce ba gaskiya ba ne a ce EFCC ta fi kauri wajen kama masu damfarar intanet.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *