Manyan Jami’an Yan Sanda 3 Sun Sami Karin Girma A Kano

Spread the love

 

Kwamishinan yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci jami’an yan sandan , da suka samu Karin girma, su kara jajircewa wajen gudanar da aiyukansu domin  nauyi ne ya karu kamar yadda suka yi alkawarin kare rayuwa da dukiyoyin al’umma.

CP Ibrahim Bakori,  ya bayyana hakan ne , a lokacin da yake likawa jami’an Karin girman, wanda aka gudanar a wajen shekatawar manyan jami’an yan sanda dake unguwar Bompai Kano.

Kakakin rundunar rundunar yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ta cikin wata sanrawa da fitar ya ce hukumar kula da aiyukan yan sanda ta kas ace ta amince da karin girman tun a ranar 20 ga watan Maris 2025 daga mukamin CSP zuwa ACP wato mataimakan kwamishinan yan sanda.

Wadanda suka samu karin girman sun hada da ACP Ahmad Munir Tudun Wada, ACP Bashir Kachalla ,
da kuma ACP Umar Mohammed Alkali.

Bakori, ya godewa babban sufeton yan sandan Nijeriya da kuma hukumar kula da aikin yan sanda ta kasa, bisa karin girman da aka yi jami’an saboda jajircewarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *