Marayu Sama Da 50 Ne Suke Korafin Matashin Da Ake Zargi Da Karbe Wayoyinsu Don Ba Su Tallafi.

Spread the love

Rundunar yan sandan jahar Kano, ta samu nasarar kama wani wani matashi mai suna Muhammad Usman, mazaunin unguwar Sharifai Kano, bisa zarginsa da damfarar marayu da sunan ba su tallafi.

Kakakin rundunar yan sandan jahar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan a lokacin da yake holen matashin, a shelkwatar rundunar dake unguwar Bompai Kano a ranar Alhamis.

SP Abdullahi Kiyawa, ya ce wanda ake zargin yana gabatar da kansa ga masu unguwani cewar shi wakili daga wata kungiya mai zaman kanta ( NGO), don samun hadinsu kan yadda za a tallafawa marayun da suka cancanta.

Idongari.ng, ta ruwaito cewa matashin yana yin yan dabaru ta hanyar karbe wayoyin hannun yan matan da akai shi gidansu don yi musu rijistar da za a ba su tallafin.

Kiyawa ya kara da cewa binciken yan sandan na farko-farko wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin, kuma an gano wayoyin salula guda 7 tare da kamo wadanda yake siyarwa.

Yan sandan sun ce yanzu haka mata sama da 50 sun shigar da korafinsu kan wanda ake zargin kuma da zarar an kammala gudanar da bincike za a gurfanar da shi, a gaban kotu don ya fuskanci hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *