Masana harkar Noma da Kiwo a arewacin Nigeria, sun Yi kira ga Manoma da su Rungumi Noman Zamani domin ya fi Noman da aka saba Yi shekara da shekaru.
Dr. Auwal Yusuf Abdullahi, Malami ne a tsangayar koyar da aikin Noma dake jami’ar kimiya da fasaha ta Aliko Dangote Kano, ne ya bayyana hakan a wata tattauna wa da idongari.ng, a karshen makon da ya gabata.
Dr. Auwal Yusuf Abdullahi, ya ce Noman da ake Yi shekara da shekaru ya Bambanta da na Zamani wajen shuka iri Mai inganci.
” Idan kasa mi iri Mai inganci guda daya Ake so ka Sanya arami , Amma a Noman baya kawai zuba wa Ake Yi kuma idan ka Sanya dayan zai Samar da yabanya Mai kyau.
Ya kara da cewa yanzu haka akwai shinkafa wadda ta ke gajeriya da kuma Mai tsayi, sannan akwai ta Tuda da kuma kwari, Wanda yakamata manomi ya Nemi malanan Gona don bayar da shawarwarin irin da yakamata a shuka.
Saurari muryar Dr Auwal Yusuf Abdullahi…
- An Karrama Mai Magana Da Yawun Gwamnan Kano Kan Batun Taimakawa Daliban Dawaki Tofa
- Likitoci a Najeriya sun shiga yajin aiki saboda sace mambarsu
” Kamar yanzu an chanja Dawar muke shukawa a baya, Inda aka Samar da Gajeriya Mai tsaba, haka kuma idan a bangaren kiwon Dabbobi ne akwai wadda akafi so domin Karan Ake so.
Dr. Auwal Yusuf Abdullahi, ya kara Jan hankalin Manoma su dinga zuwa tsangayar koyar da aikin Noma, ana Neman shawarwari don bunkasa harkar Noma da Kiwo a fadin jahar Kano da kuma Nigeria Baki daya.
A cewarsa Noma fadi ne da shi, har ya Yi kira da a koma Noma don Samar da abinci.
Haka zalika yaja hankalin hukumomin gwamnati su dinga taimaka wa Manoma da Taki, domin ya Yi tsada kuma shi ne yake taimaka wa wajen tafiyar da harkar Noman.
” Hukuma ta na fito da tsare-tsare ma su kyau kan harkar Noma Amma baya isa Hannun Manoma.
A cewar masanin duk Wanda yake zaune a karkara Babu abunda ya sani sai Noma, Amma wasu na dogara ne Kawai da Noman Damuna, Inda suke Jira sai wata Damunar ta dawo.
Ya bayar da shawarar adinga amfani da Dama-daman da ake da su , don habbaka Noman Rani da Damuna kuma kasar za ta iya daukar shukar.
Ya kuma bayyana damuwarsa kan yadda gwamnatoci ba sa bayar da kayan tallafin ga Manoma a lokacin da dace.