Mai Martaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim Abdulqadir Ya Amince Da nada Malam Ibrahim Abdullahi Suleiman a Matsayin Sabon limamin Massallacin Juma’a Na Garin Kwagwar a Karamar Hukumar Gezawa .
A Yayin da Malam Tajuddeen Ma’aruf Aminu Ya Sami Maki Casa’in da Bakwai 97% Cikin Dari a Jarabawar da aka Gudanar masu .
Wanda ‘Yan Kwamitin Tantancewar Suka Ce Malam Ibrahim Abdullahi Suleiman shi ne yai Nasarar Zama limamin Massallacin Juma’a Na Garin Kwagwar din Da Maki Casa’in da Tara Cikin Dari. 99%
A inda Malam Tajuddeen Ma’aruf Aminu zai Zama Na’ibinsa Wanda Ya Sami Maki Casa’in da Tara Cikin Dari.
Daga NanGaya, Nigeria – WikipediaYa tambayi ‘Yan Kwamitin Garin Na Kwagwar a Yankin Karamar Hukumar Gezawa cewa haka akai Suka Tabbatar da cewa haka akai,nan take Ya Bada Umarnin Aje a Nada Malam Ibrahim Abdullahi Suleiman da Malam Tajuddeen Ma’aruf Aminu a Matsayin liman da Na’ibinsa.
Kano: Yan Kasuwar Kaji Sun Koka Da Karancin Ciniki.
Dakta Aliyu Ibrahim Abdulqadir Ya Gargadi Sabbin Wadanda aka Nada da Su ci Gaba da Raya masallatansu Wajen Neman Ilimin Al-qur’ani da Sauran littatafai, tare da Zama Da Junansu Lafiya.
A Yayin da Al’umar Garin Kwagwar din Dake Yankin Karamar Hukumar Gezawa Suka tafi Garin Kwagwar Lafiya tare da Wadanda aka Nada tare Cikin Murna da farin Ciki.
Har wayau,Mai Martaba Sarkin Gaya Dakta Aliyu Ibrahim Abdulqadir Ya Tabbatar da Nada Malam Mutawakkilu Shuaibu a Matsayin Sabon limamin Massallacin Juma’a Na Garin Toronke Tsohuwa ,da Na’ibinsa Malam Shitu Munnir .
A inda Ya Kuma amince Da Nada Malam Musa Ashiru a Matsayin Sabon limamin Massallacin Juma’a Na Sabon Garin Naira Dake Gwagwarandam tare da Na’ibinsa Malam Yau Ahmadu Nasir duk a Yankin Karamar Hukumar Albasu.
- Jama’a Su Lura Da Tsaro A Filin Idi — DSS
- Ƴan sanda a Ribas sun kashe wasu da ake zargi ƴan ƙungiyar asiri