Masarautar Gaya ta kaddamar Da asusun Zakka da Waqafi Lafiya Foundation.

Spread the love

 

Mai martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim ya Kaddamar Da Asusun Neman Gudunmawa Na Zakka Da Waqafi Reshen Karamar Hukumar Gaya a jahar Kano.

Jami’in Yada Labarai Na
Karamar Hukumar Gaya
Auwalu Musa Yola, shi ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Sanarwar ta ce sarkin Gaya  Dakta Aliyu Ibrahim Wanda Ya Samu wakilcin Wamban Gaya Alhaji Mansur Ibrahim ya kuma yi  Kira ga Membobin Kwamitin Da su Tabbata Sun yi anfani da Kwarewar Da suke Da ita  a Ya yin Gudanar Da Ayyukansu, duba Da Mafi Yawansu Malamai ne a Cikin ‘Yan Kwamitin.

Da yake Jawabi tun Da Farko, Daya daga Cikin ‘Yan Kwamitin Malam Mu’azu Abdulhamid ya yi bayani mai tsawo game Da Muhimmancin bada Waqafi a Mahangar Addinin Musulunci .

Ya Kuma Kara Yin Kira ga Masu Hannu da Shuni da su  bayar Da Gudunmawarsu wajen Ganin an sauke Wannan nauyi.

Shugaban  Kwamitin Zakka Da Waqaf Lafiya Foundation Na Karamar Hukumar  Gaya Alhaji Mansur Ali Gaya ya Zaiyano wasu daga Cikin ayyukan Da Gidauniyar Zakka Da Waqaf Lafiya Foundation ya ce sun  gudanar Aikace Aikace Dan Inganta lafiyar Al-umar Yankin  Wanda Ya hada da  Horar Da Unguwar Zoma kimanin Su Talatin Da Biyar (35), Da Samar Bandakuna Da Fitulu Ga Masu  Gadin Babban Asibitin Kwararru Na  Garin Gaya, Da Sauransu.

Shima a Nasa Jawabin Shugaban Karamar Hukumar Gaya kuma mai Masaukin Baki Alhaji Ahmad T Abdullahi ya yabawa Masarautar Gaya bisa Jajircewarta Na Ganin an Kaddamar Da Asusun Na Zakka Da Waqaf Lafiya Foundation Na Yankin Dan taimakawa mabukata  dake tsakanin Al-uma Tare Da Gudanar Da Sauran Aikace Aikace Da Suka shafi rayuwar Al-umar kai tsaye .

Inda ya baiyana taron da cewa yazo a daidai lokacin da Al-uma ke Bukatarsa,tare da Jan hankalin Membobin Kwamitin Da Zakka Da Waqafi da Yankin da su yi aiki Tukuru dan Ganin an samu Nasarar da ake nema.

Sauran Wadanda suka gabatar Da Jawabai a lokacin taron sun ha da wakili daga Hukumar Gidauniyar  lafiya ,da Wakili a Hukumar Zakka Da Hubsi, da Wakili a hukumar Kula da lafiya Dake Kasar burtaniya Da Sauransu.

Taron ya samu halartar Shugabannin Kananan hukumomi Ajingi, Da Garko,da Wudil , da Dawakin Kudu,Da Gabasawa,a inda aka samu Zunzurutun Kudi Kimanin Naira Miliyan Hudu Lakadan ba Ajalan ba Nan Take.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *