Masarautar Gaya Ta Sanar Da Ganin Watan Azumin Ramadan

Spread the love

Mai Martaba Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Abdulqadir ya Bada Umarnin al’ummar Masarautar Gaya su tashi da Azumi Gobe Litinin 1 Ga Watan Ramadan Wanda yai dai dai da 11 ga Watan Maris 2024 kamar yadda fadar Mai alfarma Sarkin musulmi ya sanar da Ganin watan Ramadan.

Wannan dai na kunshe ta cikin ta cikin Wata sanarwa da Jami’in Yada Labarai Na Masarautar Gaya Auwalu Musa Yola, ya sanya wa hannu a daren Lahadi 10 ga watan Maris 2024.

Masarautar Gaya na daya daga cikin masarautu biyar dake jahar Kano.

Sarkin Gaya ya yi fatan Allah yasa mu fara lafiya, mu gama lafiya, Allah yasa mu cikin wadanda yai alkawarin “yan tawa a wannan wata Mai alfarma. Amen

An ga watan azumin Ramadan a Najeriya

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *