Masarautar Kano karkashin jagorancin Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi ii, ta Dakatar da Dagacin Garin Dogon Kawo, a yankin karamar hukumar Doguwa , Alhaji Kailani Yusuf , bisa Zargin sa da Yi wa Fulani karfa-karfar kwace Gonakinsu tare da Siyarwa.
Haka zalika ana zargin Dagacin da tursasawa ma su Gonakin sake Siyan Gonar, kuma duk Wanda ba shi da kudin sake biya, sai ya kwace ya siyarwa da Wani.
Hakanne ya sanya Fulanin da kuma mutanen Garin, suka Kai wa Hakimin Doguwa Dan-Amar Din Kano Alhaji Aliyu Harazumi, korafi kan abinda suke Zargin Dagacin da kuma hada Kai da wasu mutane don tayar da fitina a Tsakanin Fulanin kamar yadda idongari.ng, ta ruwaito.
Bayan karbar korafin ne hakimin Doguwan ya kafa kwamitin gudanar da bincike kan Zargin da ake Yi wa Dagacin Garin Dogon Kawon.
- Kotu ta hana PDP tsige Damagun a matsayin shugaban riƙo
- Ɓangarori biyu na jam’iyyar PDP sun dakatar da juna
A ranar Juma’a ne hakimin Doguwan Alhaji Aliyu Harazumi da kuma baturen Yan Sandan Doguwa , suka gudanar da taron Jin koken al’ummar yankin, Inda Dagacin Garin ya tabbatar da cewa ya aikata laifin na kwace Gonakin da kuma siyarwa, hakan ya Sanya hakimin ya bukaci Dagacin ya biya Fulanin kudadensu tare da mayar mu su da Gonakinsu.
Hakimin ya bayyana cewa yanzu haka Dagacin da ake Zargi an tube Rawaninsa, Inda aka mayar da shi wakilin Hakimin Doguwa a Garin Dogon Kawo, shi da Dan uwansa Alhaji Mustapha.
Hakimin Doguwan Alhaji Aliyu Harazumi, ya bayyana wa idongari.ng, cewa sun dauki matakin Dakatar da Dagacin Alhaji Kailani Yusuf, sakamakon korafe-korafen al’umma da ya Yi yawa.
” Shi yasa na bincika da kaina har na zo, kuma an tara mutane, don ayi komai a gabansu don gudun kar ya haifar da riciki.
Ya kara cewa sakamakon Abubuwan da suka Faru a jahohin Katsia, Zamfara da Sokoto , Inda Ake Zargin wasu daga cikin fulanin suka koma aikata laifuka, shi yasa basa fatan hakan ta kasancewa a jahar Kano.
” Mun San Fulani a kasar Kano Muna zaune da su lafiya don haka bama son zaman lafiyar ya kwace mana” .
A kowanne lokaci muna yin iya bakin kokarin mu, idan mun samu korafi daga EFCC ko bangaren Shari’a don muga an Yi adalci.
Ya kuma tabbatar da cewa kamar yadda dokar jahar Kano, ta ajiye kan rigimar kasa daman akwai kwamiti aka kafa musamman Burtalai da makiyaya, Inda Gwamnatin za ta tayar da abun Koda an Siyar abaya.
Ya kuma ja hankalin Dagatai da su kasance ma su adalci don kasa Bata siyarwa ba ce, domin Gwamnati ce ta ce bada kasa.