MASU BUKATA TA MUSAMMAN SUNA DA GATA A WAJEN MU TA KO WACCE FUSKA- SANI WAKILI.

Spread the love
Hon. Sani Adamu Wakili Ungoggo

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe, Kano.

Mataimakin shugaban kwamitin kula da masu bukata ta musamman a majalisar tarayyar kasar nan kuma dan majalisa tarayya mai wakilitar kananan hukumomin Minjibir da Ungogo, Hon. Sani Adamu Wakili, yace kwamitin nasu zai bakin kokarin sa domin ganin ya inganta rayuwar masu bukata ta musamma a kasafin kudi na shekarar badi.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da Global Track, domin bayan irin tanadin da kwamitin yayi wa masu bukata ta musamman dake fadin tarayyar kasar nan.

Sani Wakili ya kara da a duk kasafin kudi na ko wacce shekara gwamnatin tarayya tana sanya masu bukata ta musamman a cikin kushin kasafin kudin sai dai kuma basu taka kara sun karya ba, duk da cewa akwai dokar da aka yiwa masu bukata ta musamman a shekarar 2018 din data gabata domin inganta rayuwar su.

Daga cikin yinkurin da kwamitin nasu keyi na inganta rayuwar masu bukata ta musamman sun hada da samar musu da Ilimi da kuma sana’oin da zasu dogara da kan su ta yadda zasu yi goyayya da sauran al’umma dake fadin duniya.

Yana mai bayyana cewa kwamitin nasu yana sane da korafin masu bukata ta musamman na rashin saka su a cikin kunshin gwamnatoci a matakai daban daban, a inda yayi alkawarin cewa kwamitin zai yi aiki tukuru domin ganin an magance matsalar.

Dan majalisar tarayyar ya kuma sake tabbatar da cewa a yanzu haka yana ci gaba da bakin kokarin sa domin ganin ya kawo wa al’ummar kananan hukumomin Minjibir da Ungogo abubuwan more rayuwa kamar yadda yayi alkawari a lokacin yakin neman zaban sa.

Adamu wakili ya sake nanata cewa a cikin watan janairu na shekarar 2024 mai zuwa, zai kaddamar da wasu daga cikin aiyukan raya kasa daya samu daga gwamnatin tarayya wadanda suka hada da sanya fitulu masu amfani da hasken rana a kananan hukumomin guda biyu.

Hakazalika wakilin al’ummar kananan hukumomin Minjibir da Ungogo ya tabbatar da cewa nan da bada jimawa ba zai sake waiwayar batun aikin zaizayar kasa a kananan hukumomin Minjibir da Ungogo wanda a baya bayan nan hukumar kula da zaizayar kasa ta gwamnatin jihar kano da kuma na tarayya suka kai rangadi wasu daga cikin yankin da suke fada da matsalar zaizayar kasar.

Daga bisani Alhaji Sani Adamu Wakili, yace zai ci gaba tafiya da kowa da kowa domin ganin an ciyar da kananan hukumomin Minjibir da Ungogo gaba ta ko wacce fuska.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *