‘Masu garkuwa na amfani da macizai domin tsoratar da mu

Spread the love

Mutanen da suka shaƙi iskar ‘yanci daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da su sun bayyana cewa mutanen da suka sace sun a amfani da macizai masu dafi domin tsorata su.

Wasu a cikinsu da suka bayyana halin da suka tsinci kansu a ciki a hirar da suka yi lokuta daban-daban da kamfanin dillancin labarai na NAN sun ce akwai macizai masu tarin yawa a cikin dajin da ‘yan bindigar suka mamaye.

Sun ce macizan suna yawan sarar masu garkuwar da mutanen da aka sace.

Ɗaya daga cikin mutanen da ya buƙaci a sakaya sunansa ya shaida wa NAN cewa masu garkuwar sun jefa su cikin matattarar macizai.

“Masu garkuwar sun san wuraren da macizai suke kuma suna ajiye mutanen da suka sace a nan.

“Da zarar sun ga macizai, masu jin tsoronsu sai su yi ta neman guduwa. Ganin macizan na tsoratar da su.

Hukumar hisbah a Kano ta sake cafko matasa 18 ciki harda yan kasashen ketare da suka zo bikin Birthday.

Kallo ya koma sama: Kakakin kotun Musulinci a Kano Muzammil A. Fagge ya bayyana cewa ma su gabatar da kara ne suka ari Murja Kunya don tuntubarta kan wani zargi.

“Lokacin ne waɗanda aka sace suke neman ‘yan uwa da abokan arziki su sayar da komai – gida da fili da motoci da kayan gida da takalma, komai ma – kawai don a haɗa kuɗin fansa.”

Binciken da NAN ya yi ya gano dazukan da ke da mafi yawan macizai suna Birnin Gwari a jihar Kaduna da Kala-Balge kusa da tafkin Chadi a jihar Borno.

Wasu yankunan sun haɗa da Shaki a jihar Oyo da Borgu da Kagara a jihar Neja sai Karim Lamido a Adamawa da Lau a jihar Taraba.

Wasu cikin mutanen da suka kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar sun shaida wa NAN cewa lamarin ya ƙazanta a yanzu ganin yanayin zafin da ake ciki yayin da macizan ke barin ramukansu da nufin neman abinci da shan iska.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *