Masu gidajen burodi sun janye yajin aiki a Najeriya

Spread the love

Ƙungiyar masu gidajen burodi ta Najeriya (AMBCN) ta bayyana cewa ta janye yajin aikin da ta shiga bayan wata tattaunawa da ta gudanar da jami’an ma’aikatar noma ta ƙasar.

A cikin wata sanarwa da ta fitar da yammacin ranar Laraba, wadda ta samu sa hannun shugabanta, Mansur Umar, ƙungiyar ta ce ta cimma wasu yarjeniyoyi da gwamnatin Najeriya a tattaunawar tasu, wanda hakan ya sanya ta sanar da janye yajin aikin wanda ta fara a ranar Talata.

Daga cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin ƙungiyar da gwamnati sun haɗa da fitar da metric tan 25,000 na alkama nan take ga kamfanonin fulawa domin sarrafawa da samar wa masu sana’ar burodi.

Haka nan ɓangarorin biyu sun cimma yarjejeniya kan sake duba shirin samar da fulawa daga rogo da dankali da kuma dawa.

Najeriya ta sanya harajin dole ga kamfanonin da ke ɗaukar ma’aikata daga ƙetare

Gwamnatin Kano ta bankado haramtattun gine-gine 68

Sannan kuma an cimma yarjejeniyar tallafa wa masu sana’ar ta burodi ƙarƙashin wani shiri na ma’aikatar noma ta Najeriyar.

Masu gidan burodin a Najeriya sun shiga yajin aiki ne bayan kokawa da tsadar farashin kayan aiki, lamarin da ke kawo tarnaƙi a harkar sana’ar tasu.

Najeriya na fama da tashin farashin kayan masarufi, lamarin da ake dangantawa da cire tallafin man fetur a ƙasar da kuma wanu manufofi na gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *