Masu hana zanga-zanga yanzu su ne suka jagoranci ta 2012 – Atiku

Spread the love

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma mutumin da ya kara da shugaba Tinubu a zaɓen 2023, Atiku Abubakar ya ce zanga-zanga ƴancin yan ƙasa ne da ke cikin kundin tsarinmulkn Najeriya sannan kuma kotuna suka tabbatar da hakan.

Atiku wanda ya faɗi hakan a shafinsa na X ya ce “sashe na 40 na kundin tsarin mulkin Najeriya da aka gyara a shekarar 1999 ya fayyace irin ƴancin jama’a na haɗuwar jama’a.”

Mutumin da ya yi takara da shugaba Tinubu a jam’iyyar adawa ta PDP, ya ƙara da cewa ” yin bi-ta-da-ƙulli ga wasu mutane da sunan kitsa zanga-zanga wani shiri ne da ba zai nasara ba a daidai lokacin da take a bayyane cewa ƴan Najeriya da suka haɗa da masu goyon bayan shugaba Tinubu da ma jam’iyyar APC, na fuskantar yunwa da damuwa da rashin fata dangane da rashin sanin makamar wannan gwamnati.”

“Abin mamaki ne a ce mutanen da yanzu suke son daƙile ƴancin ƴan ƙasa su ne a baya suka jagoranci al’ummar aka yi zanga-zanga a 2012.” In ji Atiku Abubakar

Daga ƙarshe, tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya buƙaci gwamnati ta bai wa ƴan kƙasa damar da tsarin mulkin ƙasar ya ba su na gudanar da zanga-zangar lumana.

“Duk wani yunƙurin daƙile wannan ƴanci karan tsaye ne ga tsarin mulki wanda kuma zagon ƙasa ne ga mulkin dimokraɗiyya.” Kamar yadda ya ƙara haske.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *