Kungiyar masu sayar da magani a Kano ta bayyana ta ce sun samu wata sabuwar kasuwar da za su koma, su bar Kasuwar Sabon Gari.
Shugaban kungiyarsu, Musbahu Yahaya Khalid ya ce komawarsu sabuwar kasuwar za ta kawo karshen halin damuwa da suka shiga.
Ya bayyana haka ne a yayin da suka kai wata ziyarar duba kasuwar wacce take a Filin Dalar Gyada da ke Karamar Hukumar Dala a birnin Kano.
A cewarsa zabin da suka yi na Kasuwar Dalar Gyada ya biyo bayan sahalewar Gwamnatin Jihar Kano, don su tashi daga inda da suke a Kasuwar Sabon Gari.
- Ɓata-gari sun lalata turakun wutar lantarki, sun saka Gombe da Yola da Jalingo cikin duhu
- Mun rufe asusun banki 300 kan canjin kuɗin ƙasashen waje – EFCC
A cikin watan Fabrairu ne hukumar kula da magunguna ta kasa (PCN) tare da hadin gwiwar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna (NAFDAC) suka rufe shagunan masu ’yan maganin da ke rukunin kantinan zamani na Malam Kato da kuma Mai Karami Plaza a Kasuwar Sabon Gari, da nufin tilasta ’yan maganin komawa shagunan da aka tanada musu a Kasuwar Dangwaro da ke kan babban titin Zariya.
Hukumomin sun dauki matakin ne bayan hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Kano karkashin jagorancin Mai sharia A. T Liman ta yi, inda ta umarci ’yan maganin su koma Kasuwar Dangwaro.
Wasu daga cikinsu suka koma can, amma yawancin sauran sun yi biris da umarnin na kotu.
Shugaban, ya kara da cewa sabon wajen da suka samu ya fi na Kasuwar Dangwaro saboda hayar shagunan ta fi arha sannan yawan shagunan ya fi na Dangwaro.
- EFCC ta kama tsohon ministan sufurin jirage Hadi Sirika
- Wata Kotu Ta Yankewa Mai Cutar Yan kasuwa Da Ganyen Zogale A Matsayin Kudi Hukunci