Masu suka ku yi ta yi ko a jikina – El-Rufai

Spread the love

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya mayar da martani ga waɗanda ke caccakarsa a shafukan sada zumunta da muhawara, yana mai cewa suka da zagin da suke yi masa ba su da makama.

Tsohon gwamnan ya ce ko lama bai damu da jirkita saƙonninsa da yi msu wata fassara ta daban da ake yi ba, da cewa masu yin hakan suna yi ne cikin jahilci da son-rai.

DANDALIN KANO FESTIVAL

A jiya Asabar ne El-Rufai ya bayyana hakan a wani saƙo da ya sanya a shafinsa na X, yana mai cewa,”… abin da Allah Ya ƙaddara zai kasance, in sha Allah.”

Netizens sun yi ta caccakar tsohon gwamnan a kan wani saƙo da ya wallaf rnar Asabar da ta wuce, inda yake magana a kan ƙyashi da tsana a kan ‘yan Najeriya.

Ya yi amfani da kasancewar matimkiyar shugaban Amurka, Kamala Harris, a matsayin ƴar takarar jam’iyyar Democrat a matsayin misali na abin da yake nuni da ƙaddarar Ubangiji.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *